Tinubu ya Bukaci Majalisa ta Amince da Naɗin NJC

 

Abuja – Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta amince da naɗin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalan Najeriya (CJN).

Hakan na kunshe ne a wata wasiƙa da Tinubu ya aika kuma shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a zaman yau Talata, 24 ga watan Oktoba, 2024.

A wasiƙar, Tinubu ya faɗawa ƴan majalisar cewa sashi na 231(1) a kundin tsarin mulki ya ba shi damar nada CJN bisa shawarin majalisar shari’a (NJC), rahoton Channels tv.

Tinubu ta bukaci majalisa ta amince da naɗin NJC

Shugaban kasar ya bayyana cewa ya gamsu da nadinta bayan shawarin NJC, sannan ya bukaci majalisar dattawa da ta gaggauta tabbatar da hakan.

A ruwayar The Nation, Bola Tinubu ya ce:

“Ina gabatar maku da Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, CON domin tabbatar da naɗinta a matsayin shugabar alkalan Najeriya. Ina da yaƙinin majalisar dattawa zs ta amince da wannan buƙata.”

Takaitacccen bayani kan sabuwar CJN

Mai shari’a Kudirat mai shekaru 66 a duniya ta zama mukaddashin CJN bayan Mai Shari’a Ariwoola ya yi ritaya a watan da ya shige.

Kidirat Kekere-Ekun ita ce shugabar alkalai na 23 a Najeriya kuma mace ta biyu a fannin shari’a da ta taba kai wa wannan matsayi.

An haife ta ranar 7 ga Mayu, 1958, a birnin Landan na kasar Ingila kuma ta fara karatun shari’a ne a Jami’ar Legas inda ta samu digiri na farko a fannin shari’a a 1980.

Bayan ta kammala karatu, Kudirat Kidirat Kekere-Ekun ta zama cikakkiyar lauya a 1981.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here