Shugaba Tinubu na Shirya Yiwa Majalisar Ministoci Garambawul
FCT, Abuja – Akwai yiwuwar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yiwa majalisar ministocinsa garambawul.
Idan ba wani sauyi aka samu ba, Shugaba Tinubu zai yi garambawul ɗin ne a cikin sati mai zuwa.
Jaridar Tribune ta rahoto cewa wata majiya mai tushe a fadar shugaban ƙasa ta ce garambawul ɗin za a yi shi ne domin a kawo sababbin fuskokin da za su ƙara ɗaga darajar gwamnati.
Yaushe Tinubu zai yi garambawul?
Read Also:
Majiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar Tinubu ya yi garambawul ɗin kafin ya tafin taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA) wanda za a yi a birnin New York a cikin sati mai zuwa.
Majiyar ta ce Shugaba Tinubu yana sane da ƙorafe-ƙorafen da ake yi na rashin kataɓus ɗin wasu ministocinsa kuma a shirya yake ya sallame su.
Majalisar ta ƙara da cewa an kammala haɗa jerin sunayen ministocin da za a kora daga gwamnatin.
“Shugaba Tinubu bai gamsu da kataɓus ɗin wasu daga cikin ministocinsa ba kuma a shirye yake ya sallame su.”
“Bayan ya dawo daga taron UNGA, shugaban ƙasa zai kafa sabuwar majalisar ministoci.”
– Wata majiya
Jaridar ta ƙara da cewa wani tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari na daga cikin waɗanda ake sa ran ba muƙamin minista.