Tinubu ya yi Martani Kan Masu Zanga-Zangar Adawa da Sakamakon Zaɓe

 

Mai magana da yawun sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zargi ɗan takarar jam’iyyar adawa kan jagorantar zanga-zangar adawa sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gabatar a watan da ya gabata.

Dubban magoya bayan jam’iyyar adawa ta PDP ne dai sanye da baƙaƙen tufafi suka gudanar da zanga-zanga a ofishin hukumar zaɓe da ke Abuja babban birnin ƙasar, suna neman hukumar zaɓen da ta sake gudanar da zaɓen.

Yayin da yake mayar da martani kan zanga-zangar daraktan yaɗa labaran sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bayo Onanuga, a wata sanarwa da ya fitar ya ce zanga-zangar tamkar shure-shure ne kawai da wanda ya san ya faɗi zaɓe ke yi”, kamar yadda Jaridar Vanguard a ƙasar ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa ”ban ga ta inda zanga-zangar da Atiku ya jagoranta za ta taimaka masa wajen samun nasara shi da jam’iyyarsa”.

Atiku Abubakar, tsohon shugaban ƙasar wanda ya yi takarar shugabancin Najriya har sau shida, ya sha alwashin ƙalubalantar nasarar Tinubu a kotu, inda ya yi zargin tafka maguɗi da razana masu kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓen.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ce Tinubu ya lashe zaɓen da kashi 37 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here