Shugaba Tinubu ya Naɗa Taiwo Oyedele a Matsayin Shugaban Kwamitin Gyara Harkokin Haraji

 

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa Taiwo Oyedele a matsayin shugaban kwamitin tsare-tsare da garabawul ga harkokin haraji

Mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake ya tabbatar da wannan ci gaban a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu’a, 7 ga watan Yuli, 2023.

Tinubu ya kafa wannan sabon kwamitin ne domin magance kalubalen da suka yi katutu kan tsarin kasafi da kuma karban haraji a Najeriya.

FCT Abuja – Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da naɗin Taiwo Oyedele a mukami mai matuƙar muhimmanci.

Bayan kafa kwamitin tsare-tsaren kasafi da garambawul ɗin harokin haraji, shugaba Tinubu ya amince da naɗin Oyedele a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin.

Tinubu ya naɗa Oyedele a matsayin shugaban kwamitin gyara harkokin haraji

Hadimin shugaban kasa na fannin sadarwan zamani da dabaru, D. O Olusegun, ne ya tabbatar da haka a shafinsa na tuwita ranar Jumu’a, 7 ga watan Yuli, 2023.

Bugu da ƙari, kakakin shugaban ƙasa, Dele Alake, ya yi karin bayani kan wanda shugaban ƙasan ya naɗa a matsayin shugaban kwamitin.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Alake ya bayyana cewa:

“Mista Oyedele ya taka matsayin ƙaramin Farfesa a jami’ar Babcock University Business School.”

“Haka nan ya yi karatu a makarantun London School of Economics & Political Science, Jami’ar Yale da Harvard Kennedy School Executive Education. Lakcara ne a makarantar koyon kasuwanci ta jihar Legas.”

“Haka nan shi ne mutumin da ya kafa gidauniyar taimaka wa nahiyar Afrka (impact Africa) kuma shi ne shugaban gudauniyar.”

Shugaban ƙasa Tinubu ya amince da naɗin kwamitin ne domin cika alƙawarinsa na yaye duk wani abu da ya durkusad da kasuwanci, ya hana su bunƙasa a Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here