Tinubu Zai yi Rawar Gani Idan ya Zama Shugaban Najeriya a 2023 – Hadimin Jonathan
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Doyin Okupe yayi magana akan karfin da fitaccen jigon APC Tinubu ke da shi na mulkin Najeriya.
Okupe wanda babban hadimin shugaban kasa ne a lokacin gwamnatin Jonathan ya ce Tinubu zai zama shugaba nagari.
Sai dai, likitan da ya zama dan siyasa, ya ce bai sani ba ko shugaban APC zai samu damar zama shugaban kasa.
Lagos, Nigeria -Dr Doyin Okupe, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce Bola Ahmed Tinubu, jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, zai yi rawar gani idan ya zama shugaban Najeriya a 2023.
Read Also:
Da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Arise News a ranar Juma’a, 13 ga watan Agusta, Okupe yace Tinubu, tsohon gwamnan na jahar Legas, zai zama shugaba nagari.
Da aka tambaye shi wadanda zai yi la’akari da su idan zai yi jerin gwanayen ‘yan siyasa masu iya mulkin kasar nan, likitan da ya koma dan siyasa ya ce:
“Bola Tinubu, a wurina, zai zama shugaba nagari. Na yi imani da haka. Na yi hulda da shi.
“Wata rana na zauna tare da Bola Tinubu shekaru da yawa da suka gabata kuma ranar Asabar ce kuma babu kowa a wurin na kusan awanni huɗu kuma mun yi magana.
“Daga wannan ranar, nake girmama mutumin. Yana da nasa matsalolin, yana da nasa kurakuran amma na yi imanin idan ya samu dama zai iya yin kokari. Na yi imani da haka. “Ko zai samu dama ko ba zai samu ba, ban sani ba.”