Dalilin da Yasa Bola Tinubu ya yi Shiru Kan Rikicin Makiyaya da Manoma a Kudu Maso Yamma – Sanata Shehu Sani
Shehu Sani ya caccaki Bola Tinubu a kan ci gaba da yin shiru game da rikicin makiyaya da manoma a kudu maso yamma.
Tsohon dan majalisan ya ce Tinubu na iya rasa “takalma da hulunansa” idan ya goyi bayan wani bangare a rikicin kabilancin da ya kunno kai a Oyo da Ondo.
Ana ta rade-radin cewa Tinubu wanda ya kasance tsohon gwamnan Lagas kuma babban jigon APC yana hararar kujerar shugaban kasa a 2023.
Read Also:
Shehu Sani ya yi ba’a ga babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, a kan shiru da yayi game da rikicin Fulani makiyaya da manoma da ya kunno kai a yankin kudu maso yamma.
A wani wallafa da yayi a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairu, tsohon dan majalisan ya ce Tinubu na ci gaba da yin shiru ne a kan rikicin kabilancin da ya kunno kai sakamakon ba makiyaya wa’adin barin gari da aka yi a jahohin Oyo da Ondo saboda baya so ya “rasa hularsa.”
An zargi Fulani makiyaya da aikata laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, kashe-kashen manoma da kuma lalata gonaki a kudu maso yamma.