Rikicin Zaɓen ƙananan Hukumomi: Tinubu ya Umarci ƴansanda su Tabbatar da Tsaro a Jihar Ribas

 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kiran a zauna lafiya a jihar Rivers, inda zaɓen ƙananan hukumomi ya janyo zaman fargaba.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci ƴansanda su tabbatar da tsaro da zaman lafiya a dukkan sakatariyar ƙananan hukumomin jihar.

Wata sanarwa da mai ba shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce shugaban ƙasan ya buƙaci gwamna Siminalayi Fubara da sauran ƴan siyasar jihar Rivers zauna lafiya domin ci gaban jihar.

Shugaban ya yi wannan kiran ne bayan rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a jihar a ranar Asabar da ta gabata, inda aka samu rahoton fashewar wasu abubuwa da ƙone-ƙone bayan zaɓen.

Tinubu ya buƙaci ƴansiyasar jihar su yayyafa wa rikicin ruwa, sannan su yi kira ga magoya bayansu su zauna jihar.

“Ɗaukar doka a hannu ba tsarin dimokuraɗiyya ba ne, domin akwai kotuna da za su warware duk wata matsala.” inji sanarwar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here