Abin da Tinubu da Zaɓaɓɓun Yan Majalisar Tarayya Suka Tattauna

 

Shugaban Najeriya mai jiran gado, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sun yi wata ganawar sirri da zaɓaɓɓun ƴan majalisar tarayya na Jam’iyyar APC a Abuja, babban birnin ƙasar.

Ganarwar ta zo ne ƙasa da mako ɗaya kafin zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar jiha da za a yi ranar 18 ga watan Maris da muke ciki.

Ko da yake gabanin wannan ganawar an zaci cewa batun zaɓen wadanda za su shugabanci sabuwar majalisar dokokin ƙasar da za a kafa a watan yuni ne zai kankane ajandar taron; wasu daga cikin mahalarta taron da BBC ta tattauna da su sun ce zaman ya mayar da hankali ne kan abubuwa biyu.

Wato taya juna murnar cin zabe ganin yadda jam’iyyar ta sha ƙyar, da kuma duba yadda jam’iyyar za ta yi nasara zaɓen gwamnoni da ƴan majalisun jihohi da za a yi a ƙarshen mako.

Ɗaya daga cikin mahalarta taron kuma zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya bayyana abin da taron ya ƙunsa.

Ya ce an kira taron domin taya juna murna da kuma yin waiwaye game da irin matsalolin da aka fuskanta a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya da ya gabata domin tunkarar zaɓen da ke tafe.

A cewar Ndume, shugaban ƙasar mai jiran gado ya buƙaci a ƙyale zaɓaɓɓun ƴan majalisar tarayyar su zaɓi shugabancin majalisar ta 10 ba tare da wani katsalandan ba.

Ndume ya kuma ce taron ba shi da nasaba da batun waɗanda za a tsayar a matsayin shugabannin majalisar dokoki ta 10.

Sanatan ya kuma musanta zargin da ake cewa yana neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta gaba inda ya ce “shugabanci ɗora wa mutum a ke, shugabancin majalisa, muna jira muga abin da Allah zai yi amma babban abu shi ne a yi adalci, inda ba adalci ni bana ciki.”

A nata ɓangaren, Honorable Fatima Talba ƴar majalisa mai jiran gado daga jihar Yobe wadda ta yi nasara a zaɓen da ya gabata, ta ce ganawar na da alaƙa da batun haɗin kai sai dai ta ce yanzu hankali ya karkata ne ga zaɓen da ke tafe.

“An dai yadda mu gama wannan zaɓe da za a yi a gaba, sannan a zo a yi tunani wa ya kamata ya zama a ina.” in ji ta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here