Tireloli Sun Murkushe Masu Keke Napep, Mutane 6 Sun Mutu, 5 Sun Jikkata
Jihar Oyo – Aƙalla mutane shida ne aka tabbatar da rasuwarsu yayin da wasu mutum biyar suka jikkata a wani hatsarin da mota ya auku a jihar Oyo.
Hatsarin motan ya auku ne a kan hanyar Akanran a yankin Ona Ara a ƙaramar hukumar Ibadan da sanyin safiyar ranar Litinin.
Hatsarin mota ya auku a jihar Oyo
Jaridar The Nation ta rahoto cewa hatsarin ya auku a tsakanin wasu tireloli guda biyu da Keke Napep guda biyu.
Daga cikin waɗanda suka jikkata har da wani yaro da mahaifiyarsa ta rasu a mummunan hatsarin da ya auku.
Read Also:
Mutum biyar da suka samu raunukan sun haɗa da wasu ƴan makarantar firamare guda biyu, inda aka kai su asibitin Amuloko da ke kusa da wajen, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Yadda hatsarin ya auku
Wani ma’aikacin hukumar kula da sufuri ta jihar Oyo (OYRTMA) wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne sakamakon lalacewar birkin ɗaya daga cikin tirelolin.
“Bayan ta ƙwace sai ta danne wata Keke Napep guda ɗaya. Ɗaya tirelar wacce ke tahowa a bayanta, a ƙoƙarin kauce mata sai ta danne wata keke Napep.”
“Mun fahimci cewa mutane shida sun rasu yayin da wasu mutane biyar suka samu raunuka. Dukkaninsu an garzaya da su zuwa asibiti.”
Wani ma’aikacin OYRTMA