Trader Moni: Taimakon ‘Yan Kasuwa Don Cika Burin su
Kariyar zamantakewa hanya ce mai bangarori daban-daban da bangarorin horo daban-daban wanda ke bayar da gudummawa.
kwarai da gaske, wajan ganin cewa an rage talauci, da inganta manufofin gwamnati don ci gaba mai dorewa, Wannan yana daya daga cikin muhimman abubuwan da Ma’aikatar jin kai, Agaji da inganta rayuwar al’umma ta Tarayya, ta sa’a gaba.
Ma’aikatar na kokarin shiga rayuwar talakawa ‘yan Najeriya ta hanyar aiwatar da tsare-tsare masu dorewa, waɗanda za su taimaka wajen dakile fatara da magance kalubalen rashin aikin yi a Najeriya, tare da samar da kariya ga zamantakewa da harkokin kudi ga talakawa da marasa galihu.
Shirin TraderMoni na daya daga cikin Shirye-shiryen Ma’aikatar, Karkashin Shirin Government Enterprise and Empowerment Programmme, (GEEP), wani tsari ne da aka kirkira don bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samar da kudi ga waɗanda suke fama da talauc a Najeriya.
Shirin TraderMoni an tsara shi ne domin taimakawa kananan ‘yan kasuwa domin su fadada kasuwancinsu ta hanyar samar musu da bashi marar ruwa da lamunin kudi N50,000.
Read Also:
Shirin Trader Moni yana daya daga cikin shirye-shirye guda uku na karkashin tsarin Government Enterprise and Empowerment Programmme (GEEP), tun lokacin da aka ƙaddamar da shirin GEEP ya baiwa kananan ‘yan kasuwa sama da miliyan 2.3 rancen kudi da lamuni mara riba don su bunkasa kasuwancin su, hakan ya mai da shirin daya daga cikin manyan shirye-shirye na microcredit a duniya, da kuma shiri Mafi Tasiri fadin a Afirka, kamar yadda bakunan Afirka suka bada lambar yabo da amincewa da ita a cikin shekarar 2019 da aka gudanar a Equatorial Guinea.
Abdullahi Muhammad da ke Unguwa Uku, karamar hukumar Tarauni a jihar Kano na daya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar wannan shirin na trader moni.
Abdullahi ya shiga sana’ar kantin Provision da ke Kasuwar Tarauni, babbar kasuwa a Jihar Kano.
Ya kara da cewa;
kasuwancin nasa ya kusa karyewa saboda ba shi da jari mai karfi da zai iya faɗaɗa kasuwancin nasa da kuma siyan kayayyaki daga hannun ‘yan kasuwa, dalilin haka yasa yake amfani da karamin jarinsa wajen saye a hannun ‘yan kasuwa, ya kara ribarsa wanda hakan ya sa kayan nasa suka yi tsada.
Ya ci gaba da cewa a lokacin da ya samu labarin wannan shirin, sai ya garzaya don neman bashin mai lamunin ruwa, “abun da sauki kuma ba wahalai” in ji shi.
Abdullahi ya samu bashin da lamunin, ya sami damar amfana da Trader moni kuma ya yi amfani da shi wajen faɗaɗa kasuwancin sa, wanda a yau tsarin ya taimaka masa wajen siyan kayayyaki daga hannun mayan yan kasuwa.
“Wannan shiri na shugaban kasa Muhammadu Buhari ba kawai ya ceci kasuwanci na bane, har ma da iyalina.