Donald Trump: Shugaban Kasar Amurka Har Yanzu Yana Kan Bakarsa Na Shi Yaci Zabe
Donald Trump ya dage a kan sai ya zarce a kan kujerar shugaban Amurka.
Shugaban kasar Amurkan ya yi jawabi a Twitter, ya na cewa an yi magudi.
Trump ya ce za a gabatar da wasu hujjoji da ke nuna an murde zaben 2020.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya na nan a kan bakarsa na cewa shi ne wanda ya lashe zaben da aka gudanar a karshen shekarar 2020.
Donald Trump ya rantse cewa shi ne ainihin zababben shugaban Amurka, duk da hukuma ta tabbatar da Joe Biden ya lallasa shi a zaben bara.
A wata magana da shugaban Amurkan ya yi a shafinsa na Twitter, Trump ya bayyana cewa zai gabatar da hujjojin da za su tabbatar da gaskiyarsa.
Read Also:
Donald Trump mai shekara 74 a Duniya ya ce ya lashe zaben na 2020 da gagarumar nasara.
Da yake magana a ranar Juma’a 1 ga watan Junairu, 2020, shugaban kasar mai jiran barin gado ya yi wa dinbin masoyansa albishir da cewa zai fasa kwai.
“Za a gabatar da hujjoji rututu a ranar 6 (na watan Junairu 2020). Mun samu gagarumar nasara.”
Da yake karin bayani a ranar Lahadi, Trump ya tabbatar da cewa zai halarci gangamin da za a shirya domin nuna rashin ingancin zaben da aka yi.
Wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayyar Amurka irinsu Sanata Josh Hawley mai wakiltar mazabar Missouri sun ce ba su yarda da nagartar zaben ba.
Ko da Trump ya ke wannan magana a shafin na sa, Twitter sun ja hankalin jama’a cewa babu tabbas a game da ikirarin da shugaban Amurkan ya ke yi.