Kotu ta Tsare Matashin da ya yi Yunkurin Kashe Mahaifinsa Kan Kudi
Kotun majistare da ke Ogba a Legas ya saurari karar da ‘Yan sanda suka shigar a kan wani Innocent Osanebi.
Ana tuhumar Mista Innocent Osanebi da yin shaye-shaye, sai ya aukawa mahaifinsa, Francis Isekwene.
Jami’an ‘Yan Sanda sun ce wannan mutum mai shekara 36 ya bukaci Francis Isekwene ya ba shi kudi.
Lagos – Abin man mamaki ya faru a kararmin kotun majistare da ke zama a Ogba da ke jihar Legas da wani matashi mai shekara 36 a makon nan.
Kotun majistaren da ke Ikeja ya umarci a tsare Innocent Osanebi a gidan gyaran hali na Kirikiri a dalilin zarginsa da yunkurin kashe mahaifinsa.
Punch ta ce Mr. Innocent Osanebi ya yi wa tsohonsa mai suna Mista Francis Isekwene barazanar kashe shi da wuka a unguwar Ojodu Berger.
Mai shari’a L. A Owolabi ta zartar da hukuncin ne bayan kawo mata wanda ake tuhuma a gabanta.
Zargin yunkurin haifar da tarzoma
Read Also:
A ranar Litinin, Rundunar ‘yan sanda ta shigar da kara a kotun, ta na mai zargin wannan mai shekaru 36 a Duniya da laifin kokarin tada tarzoma.
Sufetar ‘yan sanda, Mary Adiguje ta sanar da Alkalin kotun cewa wanda ake zargi ya aikata tilon laifin ne a ranar Laraba, 1 ga watan Maris 2023.
Jaridar Nigerian Lawyer ta rahoto Mary Adiguje ta ce Innocent Osanebi ya yi wannan aika-aika ne a yayin da yake mayen miyagun kwayoyi.
Zargin da jami’an ‘yan sanda suke yi shi ne Osanebi ya sha tabar wiwi ne, sannan ya dauki wuka zuwa wajen mahaifinsa, ya na neman ya ba shi kudi.
Za a koma kotu a Afrilu
Idan ta tabbata wannan mutum ya aikata laifin da ake jifansa da shi, ya sabawa sashe na 56 na dokokin gwamnatin jihar Legas na shekarar 2015.
Da take sauraron shigar da karar a jiya, L. A Owolabi ba ta karbi rokon wanda aka yi kara ba.
Nan da kimanin makonni biyu za a koma kotun majistaren domin cigaba da shari’a, Alkali ta daga sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Afrilu 2023.