ENDSARS: Har Yanzu Ana Tsare da Wadanda Aka Kama a Lokacin Zanga-Zangar – Amnesty
Kungiyar kare hakkin dan-Adam ta duniya Amnesty International ta ce, har yanzu ana tsare da wasu daga cikin wadanda aka kama a lokacin zanga-zangar neman rushe runduna ta musamman ta ‘yan sanda masu yaki da ‘yan fashi da makami, wadda aka yi wa lakabi da ENDSARS a Lagos.
Kungiyar ta ce shekara biyu bayan zanga-zangar da aka yi a wasu sassan Najeriya har yanzu wasu daga cikin wadanda hukumomi suka kama sama da 40 na kulle a gidajen yari daban-daban na kasar.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yayin tunawa shekara biyu da zanga-zangar, yau Alhamis, Amnesty International ta ce kwamitocin da hukumomin kasar suka kafa domin gudanar da binciken cin zarafin da ‘yan sanda suka yi sun kasa tabbatar da adalci ga daruruwan wadanda aka zalunta.
Read Also:
Kungiyar da ta ce yayin da har yanzu akwai wasu gomman masu zanga-zangar da aka kama suna tsare a gidan yari, wasu daga cikinsu kuwa an gana musu azaba kafin a sake su ba tare da an tuhume su da kowa ne laifi ba.
Amnesty ta kara da cewa har yanzu ‘yan-sanda na cin zarafi da take hakkin dan-Adam har bayan zanga-zangar ta EndSars shekara biyu da wakana.
Zanga-zangar da aka yi a watan Oktoba ta watsu wasu sassan Najeriya , inda aka bayar da rahoton cewa ‘yan-sanda sun bude wuta a mashigin Lekki da ke Lagos.
Kungiyar Amnesty ta ce sojoji sun kashe mutum akalla 12 a Lekki da kuma Alausa duka a Lagos.
A kullum hukumomin kasar suna musantawa zargin kisan kiyashi da ake cewa sun yi wa masu zanga-zangar.
A sanarwara da ta fitar kungiyar ta ce har yanzu ba a aiwatar da yawancin rahotannin da kwamitocin da hukumomin kasar suka kafa domin bincke ba.
Sai dai bayanai sun nuna cewa an bai wa wasu da ‘yan sanda suka ci zarafi diyya bayan binciken da Hukumar Kare Hakkin dan-Adam ta kasar ta gudanar, wasu jami’an ‘yan sandan kuma an bayar da shawarar korarsu da gurfanar da su gaban shari’a.