Babu Tabbas ko Zan Tsaya Takara a Zaɓen 2027 – Atiku
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu tabbas ko zai tsaya takarar shugabancin ƙasar a zaɓen shekarar 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kafar talbijin ta Arise, wanda aka saki wani ɓangarenta a ranar Laraba.
An tambayi Atiku game da wanda zai jagoranci haɗakar da ƴan adawar ƙasar ke ƙoƙarin kafawa, sai Atiku ya ce tamkar abin da ya faru ne a lokacin da suka samar da jam’iyyar APC, inda bayan zaɓen fitar da gwani, dukkanin ƴan takarar suka mara wa mutum ɗaya baya, kuma ya yi nasara a babban zaɓen ƙasar.
Read Also:
Lokacin da aka tambaye shi ko zai yi takara, sai Atiku ya ce “ban sani ba, domin ya kamata ne a samar da kafa mai inganci tukuna.”
A makon da ya gabata ne Atiku Abubakar ya bayyana cewa ƴan adawa na ƙasar na tattaunawa domin yin haɗaka a ƙoƙarin tunkarar jam’iyya mai mulki a zaɓen Najeriya na 2027.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ne ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasar na 2023, lokacin da Bola Tinubu ya samu nasara.
Sai dai tun bayan kama mulkin Tinubu al’ummar ƙasar na kokawa kan tashin farashin kayan masarufi da kuma tsadar rayuwa.
Masu lura da al’amuran yau da kullum a ƙasar na alaƙanta hakan da matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka, kamar na cire tallafin man fetur da barin kasuwa ta tantance darajar kuɗin ƙasashen waje, abin da ya taimaka wajen karyewar darajar kuɗin kasar – naira.