Tserewa Daga Gidan Yari : Kusan Fursunoni 80 Sun Dawo

 

Akalla fursunoni 80 da suka tsere daga Cibiyar gyara hali ta Owerri ne suka dawo don radin kansu.

An tattaro cewa galibi wadanda suke jiran shari’, wadanda ke da karancin zaman gidan yari da kuma wadanda ke gab da kammala wa’adinsu ne suka dawo.

Sai dai kuma wata majiya ta ce tana sa ran wasu za su dawo kafin karshen mako Fiye da fursunoni 80 da suka tsere daga Cibiyar gyara hali ta Owerri sun dawo don radin kansu, jaridar The Nation ta ruwaito a ranar Laraba.

Wata majiya a hukumar gyara halayen ta Najeriya ta bayyana hakan ga jaridar.

Ya ce: “Kimanin 17 daga cikinsu sun dawo a ranar Talata sannan kuma a ranar Laraba, mun ga wasu sama da 20 sun dawo.

“Amma galibi wadanda suke jiran shari’a ne, wadanda ke da karancin zaman gidan yari da kuma wadanda ke gab da kammala wa’adinsu, sun dawo ya zuwa yanzu”.

Kimanin fursunoni 42 suka dawo a yammacin ranar Litinin, wanda ya dauki jimillan wadanda suka dawo zuwa 80.

“Matsalar da muke fama da ita, kuma bai da nasaba da fasa gidan yarin nan, shine babu wani daga cikin fursunoni masu manyan laifuka da suka tsere da suka dawo.

“Wannan abin fahimta ne saboda zai yi wuya ga mutumin da ya san cewa za a iya yanke masa hukuncin a kowane lokaci, ya dawo bayan wadanda suka kutsa cikin cibiyar sun ba shi ‘yancinsa kyauta,” in ji majiyar.

Wasu ‘yan bindiga da‘ yan sanda suka ce ’yan kungiyar IPOB ne sun kai hari a gidan yari tare da‘ yanta fursunoni 1,844 a ranar Litinin.

Ana tsammacin hakan tare da afuwar da Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar, yawancin wadanda suka tsere za su koma gidan don ci gaba da wa’adinsu.

Majiyar ta kara da cewa: “Yawancin fursunonin da suka dawo sun samu rakiyar iyayensu, lauyoyi da danginsu. “Muna sa ran wasu za su dawo nan da karshen mako.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here