Tsige Shugaba Buhari ba Shine Abinda Majalisar Tarayya ta sa a Gaba ba – Shugaban Majalisar Dattawa
Shugaban majalisar dattawa yayi fatali da kudurin da ke neman a tsige shugaba Buhari.
Ahmad Lawan ya bayyana cewa, tsige shugaban ba zai kawo karshen matsalar tsaro ba.
Ya bukaci shugaban – ta bakin wakilinsa – da ya kara dagewa wajen magance matsalar Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, ya yi watsi da batun tsige Shugaba Muhammadu Buhari da Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi game da rashin tsaro a kasar, yana mai cewa irin wannan matakin ba zai magance matsalar ba, The Guardian ta ruwaito.
Ya yi wannan tsokaci ne yayin wasan karshe na gasar kwallon kafa ta Filato ta Arewa ta farko, na hadin kai da sulhu wanda Istifanus Gyang, mai wakiltar gundumar Filato ta Arewa a Majalisar Dattawa ya shirya.
Read Also:
Lawan, wanda Sanata mai wakiltar Gundumar Benue ta Arewa maso Gabas, Gabriel Suswan ya wakilta, ya ce: “Tsige Shugaba Buhari ba shi ne abin da Majalisar Tarayya ta sa a gaba ba domin hakan ba zai iya magance matsalar rashin tsaro a kasar ba.
Sai dai ana bukatar babban kwamandan ya dauki mataki don kawar da tsoron ‘yan Nijeriya.”
A cewar Suswan, duk wani abin da ya faru na rashin tsaro da ya ci gaba, kamar abin da kasar ke gani a yau, gazawar bangaren zartarwa ne, walau a matakin jaha ko na kasa.
“Abin da muke fuskanta a yau na bukatar jajircewa daga bangaren zartarwa amma hakan na nan tafe.” Ya tunatar da Buhari cewa shi Shugaba ne na kowa, don haka, ya kamata, ya yi aiki don amfanin ‘yan Nijeriya.
Suswan yace, “Mu a majalisar kasa muna ci gaba da yin iya kokarinmu. Mun zartar da kuduri da shawarwari, amma yawancinsu ba a mutunta su ba.
Shugaban yana bukatar ya fifita fifikon Najeriya a kan kowacce,” Suswan ya nuna goyon baya ga kudiri don kafa hukuma ta musamman ta sojoji, wanda a kwanan nan ya raba kan Majalisar ta Dattawa.
Sai dai, ya ce kudirin, wanda ke neman karbar ikon nada shugabannin sojoji, daukar su aiki da kuma yi musu ritaya ta hannun shugaban kasa, ba shi da muhimmanci kamar tura sojoji don fatattakar masu tayar da kayar baya.