ALLAH ya yi wa Tsohon Gwamnan Kaduna Rasuwa – Abdulkadir Balarabe Musa

 

Tsohon gwmnan Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a safiyar ranar Laraba a gidansa da ke Aliyu Turaki Road Unguwar Sarki Kaduna.

Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya kuma za ayi jana’izarsa a yau Laraba Rahotannin da muka samu ta tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan Jihar Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa.

‘Yar marigayin ta tabbatar da cewa ya rasu a safiyar ranar Laraba a kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A cewarta, za ayi masa jana’iza a yau da rana.

Tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani shima ya sanar da rasuwar tsohon gwamnan a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba.

A sakon da ya wallafa a Twitter, Shehu Sani ya rubuta “Alhaji Balarabe Musa ya rasu a yau. Allah ya jikan rai ya kuma saka masa da gidan Aljanna Firdausi. Amin.”

Balarabe Musa ne gwamna na farko da aka fara tsige wa a tarihin Najeriya.

Har wa yau, shine shugaban jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP) a jamhuriyya ta hudu amma ya sauka daga mukamin a shekarar 2018 saboda ya kula da lafiyarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here