Tsohon Gwamnan Legas da Kuma Imo Ya Rasu
Tsohon gwamna a mulkin soja, Ndubisi Kanu, ya mutu yana da shekaru 77 a duniya.
A lokacin yana soja, Kanu, ya yi gwamna a jahohin Legas da kuma Imo.
Bayan Kanu ya yi murabus daga aikin soja, ya zama mai rajin kare hakkin bil adama.
Tsohon gwamnan jahohin Legas da Imo a zamanin mulkin soja, Rear Admiral Ndubisi Kanu (mai murabus) ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.
Read Also:
Abokiyar huldar Kanu kuma mukusanciyarsa, Mrs Joe Okei-Odumakin ta tabbatar wa The Punch labarin a ranar Laraba.
“Tabbas ya rasu. Wannan labari ne na bakin ciki.
Za mu fitar da sanarwa nan bada dadewa ba,” in ji ta. A halin yanzu ba a iya tabbatar da sanadin rasuwarsa ba.
Kanu, wadda tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Murtala Mohammed ya nada cikin majalisar kolin sojoji a shekarar 1975, daga bisani ya zama mai rajin kare hakkin bil adama bayan barin aikin soja.
Ya shiga kungiyar kare demokradiyya ta NADECO, sannan ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin an soke zaben shugaban kasa na June 12 a shekarar 1993.