Bayan Watanni a Gidan Kurkuku: Tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP ya Samu ‘Yanci

 

Tsohon kakakin jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, ya bar gidan yarin Kuje bayan ya shafe watanni goma.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Metuh a gaban kotu bisa zarginsa da karbar miliyan 400 daga ofishin Dasuki ta haramtacciyar hanya.

Olisa Metuh, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP, ya shaki iskar ‘yanci bayan y shafe watanni goma a gidan yari.

Gidan talabijin na Channels ya nuna hotunan Metuh yayin da ya ke barin gidan yari na Kuje a Abuja, babban birnin tarayya.

Channels ta bayyana cewa jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ne ya fara wallafa hotunan Metuh na barin gidan yari a shafinsa na tuwita.

Fayose ya taya Metuh murnar samun ‘yanci inda ya bayyana cewa, “barka da dawowa gida Olisa Metuh, komai tsananin wuya, sauki na biye da ita…..”

Hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci, ita ce ta fara gurfanar da Metuh tare da wani kamfani, Destra Investment Limited a gaban mai shari’a Jastis Okon Abang na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Ana tuhumar Metuh da laifin karbar kudi har miliyan dari hudu ta haramtacciyar hanya daga ofishin tsohon ma bawa shugaban kasa a harkar tsaro (NSA), Kanal Sambo Dasuki.

A ranar 25 ga watan Fabarairu na shekarar 2020 ne mai shari’a Abang ya zartar da hukuncin daurin shekaru bakwai ga Metuh.

Metuh ya garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin da kotun da ke kasanta ta yanke masa.

Watanni goma bayan daukaka karar, kotun koli ta amince da dalilan Metuh tare da warware hukuncin da kotun farko ta zartar da kuma bayar da umarni a sake shigar da sabuwar kara a kansa.

An saki Metuh daga gidan yarin Kuje sati daya bayan kotun koli ta warware hukuncin kotun farko.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here