Kudi Wata Tsutsuwa Akan N729 Miliyan

Tseren tsuntsaye yana daya daga cikin wasanni a kasar Belgium.

Masu siyar da tsuntsayen tseren suna ta samun dumbin dukiya.

Ana sayar da tsuntsu mai shekaru 2, a kalla N729,479,670.40 An sayar wa wani dan kasar China da wata tsuntsuwa wacce suke kira New Kim a ranar Lahadi.

A kasar Belgium, ana sayar da tsuntsuwar tsere, wacce suke kira da New Kim a kalla euros miliyan 1.6, wanda yayi daidai da N729,479,670.40.

Wani babban dan kasuwa mai harkokin tsuntsaye ya siyar da tsuntsun a wani taro da aka yi ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, kamar yadda Indian Express suka ruwaito.

Shugaban kungiyar sayar da tsuntsayen, Pascal Bodengien, ya ce mutane su na tururuwar zuwa siyan tsuntsaye a wurinsu.

Bodengien ya yi na’am da babban cigaban da suka samu na siyar da tsuntsu daya a euro miliyan 1.6, ya kuma ja kunnen masu son shiga harkar wasan don samun kudi su sabunta tunaninsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here