Soke Harajin Tsaron Intanet: TUC ta yi Barazanar Gudanar da Zanga-Zanga
Ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Najeriya ta yi barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga tare da dakatar da al’umura a faɗin ƙasar matuƙar gwamnatin tarayya ba ta soke sabon harajin tsaron intanet da Babban bankin ƙasar ya ɓullo da shi ba.
Ƙungiyar ta yi barazanar ce a wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar, Festus Osifo.
Read Also:
Hakan na zuwa ne bayan ita ma ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta soki lamirin sabon harajin, wanda ta bayyana a matsayin wani gagarumin nauyi da gwamnati ke ɗora wa talaka.
A ranar Talata ne Babban Bankin Najeriya ya fitar da wata sanarwa wadda ke neman a cire harajin kashi 0.5 cikin ɗari kan duk wata hada-hadar tura kuɗi da mutanen ƙasar suka yi ta intanet.
Sanarwar TUC ta ci gaba da cewa “babu dabara wajen fito da irin wannan haraji daidai lokacin da ƴan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa sanadiyyar faɗuwar darajar naira da ƙarin farashin man fetur da na lantarki.