Jovenel Moise: Ana Tuhumar Firaministan Haiti, Ariel Henry kan Mutuwar Tsohon Shugaban ƙasar
Wani mai shigar da kara a Haiti ya gabatar da wata kara wadda a ciki ya ke tuhumar firaministan ƙasar Ariel Henry da hannu cikin kisan gillar da aka yi wa shugaban ƙasar Jovenel Moise a watan Yuli.
Read Also:
Wannan matakin ya biyo bayan matakin da babban mai shigar da kara na ƙasar Bedford Claude ya dauka na neman Mista Henry ya bayyana alakarsa da mutumin da ake tuhuma da bayar da umarnin kashe shugaban ƙasar.
Ya ce bayanan da wani bincike ya bankaɗo sun tabbatar cewa mutanen biyu sun tattauna da juna har sau biyu jim kadan bayan an kashe Mista Moise.
Mutuwarsa a gidansa da ke wajen birnin Port-au-Prince ya haifar da wata matsalar siyasa wadda gagarumar girgizar ƙasar da aka yi a watan jiya ya kara dagula lamurra a Haiti.
A dalilan wannan karar an hana Mista Henry barin kasar.