Tukunyar Iskar Gas ta Fashe a Jahar Legas
Tukunyar iskar gas ta fashe ta yi ‘bindiga’ a Agboju a jahar Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon fashewar.
Hukumar LASEMA ta jahar Legas ta tabbatar da afkuwar lamarin kuma ta tura jam’anta An samu fashewar gas a karamar hukumar Amuwo-Odofin na jahar Legas a ranar Talata 12 ga watan Afrilun shekarar 2021, The Punch ta ruwaito.
An gano cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon lamarin da ya faru a layin Iyasoko da ke Agboju, Amuwo-Odofin.
Read Also:
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 6.55 na yamma. Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa na Legas, LASEMA, Nosa Okunbor ya tabbatar da fashewar gas din inda ya ce an tura jami’ai masu ceto zuwa wurin misalin karfe 6.50 na yamma.
Ba a tantance adadin mutanen da goborar ta shafa ba a lokacin hada wannan rahoton. Ya ce, “Eh, da gaske ne. Tawagar jami’an mu suna hanyarsu na zuwa wurin.
Cinkoson ababen hawa ne ya sa suka yi jinkiri. Ba zan iya tantance irin barnar da ta faru ba a yanzu.” Ku saurari karin bayani …