Fasto Tunde Bakare ya Shawarci Shugaba Buhari Akan Gwamnatinsa
Kalaman da Tunde Bakare ya yi kwanaki a kan mulkin Buhari sun jawo surutu.
A hudubarsa ta makon nan, Fasto Tunde Bakare ya ba shugaban kasa shawara.
Bakare ya ba Muhammadu Buhari shawara ya sallami wasu da ke gwamnatinsa.
Legas – Tunde Bakare, wanda ke limanci a cocin Citadel Global Community Church, ya sake tofa albarkacin bakinsa kan gwamnatin Muhammadu Buhari.
Fasto Tunde Bakare yace ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zazzaga a gwamnatinsa, maimakon ya rika sukar gwamnatocin baya.
Jaridar The Cable ta ce malamin addinin kiristan ya yi wannan bayani ne a hudubar da ya yi wa mabiyansa a ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli, 2021, a coci.
Faston yake cewa kalaman da ya yi a makon da ya wuce, na sukar gwamnatin APC sun jawo surutu daga bakin jama’a – har da abokai da na kusa da shi.
Tunde Bakare ya yi wa jama’a godiya
Read Also:
“Abubuwa sun yi mani nauyi daga kusa da nesa a makon da ya shude, daga manyan mutane saboda sakon da na fitar a ranar Lahadin da ta wuce.”
“Bayan wayoyi na da aka yi ta kira babu kaukauta wa, wasu sun ziyarce ni har gida domin jin abin da ya faru da abokantaka da shugaban kasa.”
“Gaskiya na ji dadin damu war da ‘yanuwa, abokai da abokan aiki suka nuna, musamman wadanda suka dage wajen addu’o’in kariya daga makiya.”
Shugaban kasa ya kawo sababbin hannu a shekarar bana
“A madadin a rika sukar wadanda suka ci amanar rikon shugabancin da aka ba su, abin da ya dace ga shugaba shi ne ya gano mutanen nan, sai ya yi waje da su.”
“Shiyasa ake da bukatar ya yi zazzaga a gwamnatinsa, ya kawo sababbin hannu a shekara 2021.”
Fasto Bakare ya ce ya yi amfani da duk wata dama da ya samu a fili ko a sirri wajen ba mai girma shugaban kasa shawara, kuma zai cigaba da yin hakan har gobe.