Kungiyar Kwadagon Tunusia ta yi Kira ga ‘Yan Kasar da su Tsunduma Yajin Aiki Domin Kalubalantar Shugaban ƙasar
A wani mataki na karuwar kalubale ga shugaban Tunisia, Kais Saied, ma’aikatan gwamnati za su tsunduma yajin aiki a daukacin kasar.
Kungiyar kwadagon Tunusia ta yi kira ga ‘yan kasar, su fito zanga-zangar kin amincewa da matakan da shugaba Saeid ke dauka na farfado da tattalin arzikin kasar.
Read Also:
A yanzu shi ke jan ragamar majalisar da ya tarwatsa a shekarar da ta gabata, kuma ‘yan kwadago sun ki amincewa su shiga shirinsa na sauya kundin tsarin mulkin Tunisia.
Ministan ayyuka Nasreddin Nsibi, ya shaidawa kafar yada labaran kasar, yaji aikin zai janyowa Tunisia asarar miliyoyin daloli, a daidai lokacin da tattalin arzikinsu ya faɗa halin ni ‘ya su.
A ɓangare guda kuma gwamnati na cewa ta na tuntubar masu bada bashi na kasashen waje, domin samar da alkama, da magunguna da fan fetur.