Zanga-Zangar ‘Yan Kwadago: Sifeto Janar na ‘Yan Sanda ya Tura Jami’an ‘Yan Sanda Jahar Kaduna
Shugaban ‘Yan Sanda na kasa ya tada Dakaru na musamman zuwa Kaduna.
IGP Usman Alkali Baba ya bada umarnin a tabbatar da zaman lafiya a jahar.
Hakan na zuwa ne bayan an soma yajin-aiki, ana ta zanga-zanga a Kaduna.
Mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya umarci dakarunsa da cewa ka da su bari wani rikici ya barke a fadin jahar Kaduna.
A ranar Litinin, 17 ga watan Mayu, 2021, Usman Alkali Baba ya bada umarnin a kare rai da dukiyar mutane yayin da aka soma yajin-aiki a Kaduna.
IGP Usman Alkali Baba ya bada wannan umarni ne yayin da kungiyoyin kwadago suka soma yi wa gwamnatin Nasir El-Rufai zanga-zanga da yajin-aiki.
Read Also:
Umarnin da Usman Alkali Baba ya ba ‘yan sandan ya shiga hannun Daily Trust jim kadan bayan kungiyoyin kwadago sun dakatar da ayyuka a Kaduna.
Sufetan ‘yan sandan yake cewa ya zama dole a baza jami’an ‘yan sanda na musamman domin a karfafa tsaro a kan hanyar Kaduna zuwa birnin Abuja.
Babban jami’in da ke kula da yada labarai da hulda da jama’a na ‘yan sanda na kasa, Frank Mba, ya fitar da wannan jawabi, ya na sanar da AIGs da CPs. Frank Mba ya sanar da manyan jami’an ‘yan sandan su tabbatar da zaman lafiya a yankunansu.
Ya ce: “Bayan haka, IGP ya umarci AIG (mataimakan sufetocin ‘yan sanda) da kwamishinonin da ke jahohi da shiyyoyi da ke kula da hanyoyin Kaduna-Abuja da kewaye, su kare rai da dukiyoyin al’umma da ke karkashin duk yankunan da suke da iko.”
Umarnin ya ba jami’an kar-ta-kwana umarni su shiga jahar Kaduna, da nufin tabbatar da tsaro.
“Haka zalika, mataimakin sufetan ‘yan sanda da ke kula da sashen samun bayanan sirri, ya bada umarni ayi maza a baza dakarun IRT da STS.” Inji Mba.