ƙasashen Nahiyar Turai ba su da Wani Zaɓi Illa su Ci gaba da Amfani da Fetur da Gas ɗin ƙasata – Shugaban Rasha
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasashen nahiyar Turai ba su da wani zaɓi illa su ci gaba da amfani da fetur da gas ɗin ƙasarsa, yana mai gargaɗin “halin ƙunci na tattalin arziki” idan suka yi yunƙurin maye gurbin makamashin nasa da wani.
Read Also:
“Turai ba su da wani zaɓi cikin sauƙi,” a cewar Putin cikin wata hira da manema labarai ta bidiyo daga gidansa da ke kusa da birnin Moscow ranar Alhamis.
“Babu tarin man a kasuwar duniya, kuma na ƙasashen duniya, kamar Amurka, da ake tunanin kaiwa Turai, zai yi wa masu amfani da shi tsada matuƙa.”
Tuni ƙasashen Turai suka fara tunanin rage dogaro da makamashin Rasha.
Shuagaban Ukraine Zelensky ya sha sukar ƙasashe kamar Jamus da suka hana a saka takunkumi kan makamashin na Rasha, suna masu cewa zai shafi rayuwar al’ummar ƙasashen nasu.