Turkiyya: Girgizar ƙasa ta Kashe Wasu Mutane a Kasar

 

  Masu aikin ceto a birnin Izmir na Turkiyya sun kwana suna hako bululluka masu ƙwari a cikin duhu domin lalubo wadanda ke da sauran numfashi bayan girgiza kasa ta afkawa Aegean a jiya Juma’a.

   Magajin garin Izmir Tunc Soyer yace gine-gine 20 suka rushe, masu aikin agaji sun bada rahoton mutuwar mutane 20, dari 7 kuma sun samu rauni.

Girgizar kasar mai karfi maki 7 ta kuma lalata tsiribin Samos na Girka da ke kusa, da sanadi rayukan yara 2 bayan katanga ta rufta musu.

Guguwar ta kuma haddasa tumbatsar teku inda ruwa ya malala a tittuna unguwannin da ke kuda da tashar jirgi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here