Kamfanin Uber ya ƙaddamar da Baburan Haya Masu Amfani da Lantarki a Kenya

 

Kamfanin Uber da ke gudanar da hayar abubuwan hawa a shafin intanet, ya ƙaddamar da baburan haya masu amfani da lantarki a birnin Nairobi na ƙasar Kenya, a wani abu da kamfanin ya ce shi ne na farko a Afirka.

Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin ƙasar ke shirin fara amfani da motocin lantarki a ƙasar, a wani ɓangare na rage gurɓata muhalli.

kamfanin Uber ya ce da farko zai gabatar da baburan 3,000 waɗanda za su iya ɗaukar diraba da fasinja ɗaya.

Bankin Duniya ya yi ƙiyasin cewa sana’ar Achaɓa ko fannin baburan haya a Kenya na samar da ayyukan yi ga mutum fiye da miliyan 1.5, tare da tallafa wa tattalin arzikin ƙasar da fiye da dala biliyan 1.4 a kowacce shekara.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com