An Samu Na’ukan Cutar Polio Guda 70 a Jihohi 14 na Arewacin ƙasar – Gwamnatin Najeriya
Najeriya na fuskantar ƙaruwar yaɗuwar sabuwar na’uin cutar polio ta cVPV2, kamar yadda Hukumar Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta bayyana.
Babban daraktan hukumar, Dokta Muyi Aina ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a wani taro da ya yi da shugabannin addini, wanda hukumar ta shirya tare da haɗin gwiwar Gidaunar Sultan wato Sultan Foundation for Peace and Development.
Read Also:
Ya ce an samu jimillar na’uin 2 cVPV2 guda 70 a ƙananan hukumomi 46 a jihohi 14 na arewacin Najeriya.
A cewarsa, “wannan na nuna cutar na cigaba da yaɗuwa saboda ƙarancin aiwatar da allurar riga-kafi. Dole a canja wannan tsarin. Dole mu tabbatar kowace mace ta samu kula a lokacin da take ɗauke da juna biyu, sannan ya zama ƙwararru ne suke amsar haihuwa, sannan mu tabbatar kowane jariri na kammala allulorinsa na riga-kafi kamar yadda aka tsara.”
Ya yi kira ga shugabannin addini da su ƙara ƙaimi domin tabbatar da shirin allurar riga-kafi na tafiya daidai.