Ukraine ta yi iƙirarin Harin da ta kai Sevastopol ya Kashe Kwamandojin Rasha

 

Ukraine ta ce harin makami mai linzamin da ta kai tashar jiragen sojin ruwan Rasha a gaɓar tekun Bahar Aswad a yankin Crimea ya zo daidai da lokacin da kwamnadoin sojin ruwan Rasha ke yin wata ganawa.

Cikin wata gajeriyar sanarwa da sojojin Rasha suka fitar, sun yi iƙirarin cewa harin ya haddasa mutuwar sojojin tare da raunata wasu da dama, sai dai sanarar ba ta yi ƙarin haske ba.

A ranar Juma’a ne Rasha ta ce ɗaya daga cikin sojojin ruwanta ya ɓace bayan harin.

An kallon tashar jiragen ruwan – wanda ke birnin Sevastopol – a matsayin rundunar sojin ruwan Rasha mafi ƙarfi.

Wata majiyar sojojin Ukraine ta shaida wa BBC ta kai harin ne ranar Juma’a ta hanyar amfani da wasu makamai masu linzami da Birtaniya da Faransa suka samar wa ƙasar.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com