Gwamna Umahi ya Bada Umarnin Kama ‘Dan Takara da Shugaban Jam’iyyarsa Kan Kashe Mutane
David Umahi ya ziyarci Ekoli Edda a karamar hukumar Afikpo bayan kisa da kone-konen da aka yi.
Gwamnan Ebonyi ya bada umarnin gaggawa cewa a damke shugaban APC da ‘dan takarar jam’iyya mai-ci.
Ana zargin shugaban APC na jihar Ebonyi, Stanley Okoro Emegha ya na da hannu a abin da ya faru a kauyen.
Ebonyi – A ranar Talata, 27 ga watan Disamba 2022, Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bada umarni a kama shugaban APC, Stanley Okoro Vanguard ta ce ana zargin Mista Stanley Okoro Emegha da hannu a mutuwar mutane da kuma kona gidajen jama’a da aka yi a Ekoli Edda da ke garin Afikpo.
Baya ga haka, Mai girma Gwamnan ya kuma bada umarni ayi gaggawar cafke Eni Uduma Chima mai neman takarar ‘dan majalisar tarayya na yankin Afikpo.
Gwamnan ya bada wannan umarni ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido bayan harin da aka kai wa mutanen kauyen Ekoli Edda, har aka kashe mutane uku.
Read Also:
Ana zargin Emegha.da Chima da laifi A rahoton Daily Post, an ji cewa ana zargin wadannan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki su na da hannu a kan abin da ya faru, don haka za a bincike su.
Gwamnan ya fitar da jawabi ta bakin Chooks Oko wanda shi ne Mai taimaka masa wajen yada labarai da dabaru, ya bukaci a kama duk wadanda ake zargi.
Jawabin da Chooks Oko ya fitar David Umahi ya bada umarnin ayi gaggawar kama Shugaban APC, Stanley Emegha da ‘dan takara, a kan rawar da suka taka wajen kashe mutane uku a Ekoli Edda.
mahi ya umarci Kwamishinan ‘yan sanda ya kama duk wadanda ake zargi su na da hannu a wannan aika-aika da aka yi, domin a tabbatar doka tayi aiki a kansu.
– Chooks Oko
A jawabin, Gwamnan Ebonyi ya dakatar da yin duk wani taron jama’a a Ekoli Edda har sai zuwa lokacin da zaman lafiya da kwanciyar hankali su ka dawo.
Tribune ta ce yanzu jami’an ‘yan sanda da sojoji da dakarun Ebubeagu sun zagaye kauyen domin gudun abin da ya faru ya sake maimaita kan shi a nan gaba.
Abin da ya faru – Kwamishinan ‘yan sanda Ana haka ne Kwamishinan ‘yan sanda na Ebonyi, Aliyu Garba ya tabbatar da mutuwar mutane uku a sakamakon tada-zaune-tsayen da aka yi a jihar.
CP Aliyu Garba ya fitar da jawabi a Abakaliki, ya ce rikicin da ya barke tsakanin mutanen Chima Eni da Stanley Emegha ne ya jawo aka rasa rayuka a jihar.