‘Yan G5 Sun Karkata  Kan ‘Yan Takara 2 a Zaben 2023

 

Gwamnoni 5 da suka yi fito-na-fito da Atiku Abubakar a PDP za su goyi bayan wani ‘dan takara dabam.

Ana tunani ‘Yan G5 za su fadawa magoya bayansu su zabi Peter Obi ko Bola Tinubu ne a zabe mai zuwa.

Da alama Olusegun Obasanjo yana goyon bayan Obi, wasu kuma sun fi ganin cin ta ga jam’iyyar APC.

London – Alamu masu karfi su na nuna Gwamnonin PDP biyar da ba su goyon bayan takarar Atiku Abubakar za su bayyana matsayarsu a kan zaben 2023.

Rahoton Punch na ranar Laraba, 28 ga watan Disamba 2022, ya nuna nan da 5 ga watan Junairun 2022, Gwamnonin jihohin za su sanar da ‘dan takaransu.

na tunanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo zai iya tasiri a kan zabin wadannan gwamnoni da yanzu su na taro a birnin Landan a Birtaniya.

Cif Olusegun Obasanjo yana da ra’ayin cewa kamata ya yi mulkin Najeriya ya koma yankin Kudu maso gabas a badi, ana zargin yana goyon bayan Peter Obi.

Obasanjo ya dage a kan LP

Watanni hudu da suka wuce, Obasanjo wanda ya mulki kasar nan tsakanin 1999 da 2007 ya zauna da wadannan Gwamnoni a Landan, ya tallata masu Obi.

Peter Obi yana neman takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar hamayya ta LP. A cikin manyan ‘yan takaran 2023, shi kadai ya fito daga Kudu maso gabas.

Hadimin wani daga cikin ‘Yan G5 ya shaidawa Punch cewa wasu daga cikin Gwamnonin nan na duba yiwuwar bin shawarar tsohon shugaban Najeriyar.

A ba Ibo mulki a 2023

Obasanjo yana ganin idan daga Kudu za a fito da shugaban kasa, kamata ya yi a je Kudu maso gabas, yankin da bai taba samun damar rike shugabanci ba.

Majiyar ta ce wannan shi ne abin da ya sa Obasanjo ya zauna da Gwamnonin a Landan a watan Agusta. A gefe guda ana tunanin wasu na goyon bayan APC.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here