NARD: Kotun NIC ta Umarci Kungiyar Likitoci da ta Dakatar da Yajin Aiki

 

Abuja – Kotun ma’aikata ta kasa dake zamanta a Abuja (NIC) ta umarci kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta dakatar da yajin aikin da take.

Alkalin kotun, John Targema, shine ya bada wannan umarnin yayin da yake yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar, kamar yadda the cable ta rawaito.

Punch ta rawaito cewa Likitocin sun tsunduma yajin aiki a ranar 1 ga watan Agusta kan rashin biyansu albashi yadda ya kamata da sauran wasu dalilai.

Alkalin kotun yace:

“Bayan duba da kuma nazari kan rantsuwa da kuma bukatar gaggawa da masu shigar kara suka gabatar.

Kotu ta auna kuma ta yi biyayya ga dokoki kamar yadxa aka gabatar mata.”

“Ina bada umarnin cewa a dakatar da duk wata rashin jituwa tsakanin mai shigar da kara da kuwa waɗanda ake kara yayin da za’a cigaba da sauraron shari’ar zuwa karshe.”

Kotu ta ɗage sauraron karar har zuwa Satumba

Alkalin ya kara bada umarni ga waɗanda ake kara su tabbatar sun dauki.mataki game da hukuncin da aka yanke kafin zama na gaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here