IGP Usman Alkali ya ba da Umarnin Sauya Fasalin Tsaro a Anambra 

 

Sifeta Janar na ƴan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya ba da umurnin sauya fasalin tsaro a jahar Anambra.

Umurnin na IGP Alkali na zuwa ne a dai-dai sadda ake shirin gudanar da zaben gwamna a jahar ranar 6 ga watan Nuwamba.

Sauye-sauyen za su shafi masu gogaggun kwamandoji da suka kai muƙamin mataimakin kwamishina ƴan sanda, da za su sa ido kan yadda jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu a zaben.

Ana shirin gudanar da zaben na 6 ga watan Nuwamba a Anambra a dai-dai lokacin da mambobin kungiyar yan aware ta IPOB ke ci gaba da tada zaune tsaye a yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here