ICRC ta Bayyana Cewa Sama da Mutane 20,000 Suka ɓata a Arewa Maso Gabashin Najeriya

 

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce sama da mutum 20,000 ne suka yi sama ko kasa saboda rikicin da ke faruwa a arewa maso gabashin Najeriya.

ICRC ta ce yakin wanda aka shafe shekara 12 ana yi ya sa an yi asarar dubban rayuka, kuma miliyoyi sun rasa matsugunansu.

A wani taron masu ruwa da tsaki da take gudanarwa a Maiduguri, ICRC ta ce ta yi rijistar sama da mutum 20,000 da suka ɓata a arewa maso gabas, kuma suna fargabar cewa ko dai sun tsere ko kuma an kashe su.

“A karamar hukumar Bama kawai mun yi rajistar mutum 4,000 da ba a san inda suke ba a halin yanzu”, in ji Usman Kunduli Bukar na kungiyar ta Red Cross.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here