Shugaban Venezuela ya Sanar da Zaman Makokin Kwana Uku Bayan Ambaliyar Ruwa ta Halaka Mutane 25 a Kasar

 

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ayyana zaman makokin kwana uku bayan mamakon ruwan sama da ya halaka mutum aƙalla 25.

Ruwan saman ya haifar da ambaliyar ruwa a tsakiyar ƙasar.

Mataimakiyar Shugaban ƙasar, Delcy Rodriguez ta ziyarci ɗaya daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi shafa.

Miss Rodriguez ta bayyana cewa mutum 52 ne ba a san inda suke ba.

Dubban ma’aikatan agaji ne kuma ke ci gaba da gudanar da aikin ceto.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here