Kadan Daga Cikin Wadanda Suka Rasa Rayukansu a Harin Jirgin Kasa na Abuja-Kaduna

A ranar 28 ga watan Maris ɗin 2022 ne wasu ƴan bindiga suka dasa bam a kan hanyar da jirgin ƙasa yake wucewa daga Abuja zuwa Kaduna.

Bayan da bam ɗin ya tilasta wa jirgin tsayawa ne a ranar Litinin da daddare, sai kuma maharan suka fara harbin kan mai uwa da wabi – inda wasu bidiyo da mutane suka yaɗa a intanet suka nuna yadda wani sashe na jirgin ya yi fata-fata, da wasu gawarwaki a kwance sannan da kuma wasu da suka jikkata.

Rahotannin farko-farko sun ce fasinjoji 970 ne a cikin jirgin, amma kwana biyu bayan nan sai gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da sanarwar cewa bayanan da ta samu daga Hukumar Kula da Jiragen kasa ta Najeriya NRC sun nuna cewa mutum 362 na a ciki.

A yanzu dai ƴan Najeriya da dama sun fi amfani da jirgin ƙasa wajen tafiya daga Abuja zuwa Kaduna maimakon bin mota, saboda yadda ƴan bindiga ke sace mutane a kan titin.

Mutane da dama sun fi son bin jirgin ƙasan saboda tsaro.

Bayanan baya-bayan nan sun ce hukumar agajin gaggawa ta Jihar Kaduna ta ji ta bakin iyalai don samun bayanai a wajensu kan fasinjojin da suka yi tafiya a ranar.

Ga dai wasu daga cikin waɗanda aka samu tabbacin mutuwarsu.

Farida S Mohammed

Duk da cewa dai BBC ba ta samu yin magana da dangin Farida S Ibrahim ba, amma labarin rasuwarta a cikin harin jirgin ya yadu a kafafen sada zumunta.

Kamar yadda bayananta a shafinta na Tuwita suka nuna Farida lauya ce kuma ma’aikaciyar banki.

Wani ɗan uwanta ya wallafa labarin rasuwar tata a shafinsa na Tuwita.

Ya ce da fari sun yi ta neman ji daga gare ta amma ba su samu ba, sai daga baya da hankula suka lafa aka gano gawarta.

Sannan bayan wannan saƙon ya sake wallafa wani da ke cewa: “Assalamu Alaikum. Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.

“Za a yi jana’izar Farida S Mohammed bayan Sallar La’asar a Masallacin Juma’a na Yahya Road in Allah Ya yarda. Allah Ya ji kanta Ya gafarta mata.”

Abdu Isa Kofar Mata

Abdu Isa Kofar Mata kafin rasuwarsa darakta ne a hukumar kula da iliin fasaha.

Wani ƙaninsa Mukhtar ya shaida wa BBC cewa ya rasu ne sakamakon harbinsa da aka yi, “lamarin da ya ɗimauta iyalansa.”

An bayyana shi a matsayin mutum mai tausayin mutane da taimako.

Dr Chinelo Nwando

Wata likita ƴar Kanada Chinelo da ke aiki a asibitin St Gerald a Kaduna ta rasa ranta a harin.

Sakatariyar Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya NMA, reshen Jihar Kaduna, Aisha Mustapha ta tabbatar da mutuwar Dr Chinelo, inda ta ƙara da cewa likitar na da shirin tafiya Kanada a ranar Juma’a kafin wannan harin da ya ɗauki rayuwarta.

NMA ta bayyana likitar a matsayin mai sadaukarwa a kan aikinta ta kuma ce tabbas za a yi kewarta.

An yi ta alhinin mutuwarta a shafukan sada zumunta inda mutane suka yi ta bayyana ta a matsayin mai nutsuwa da kirki.

Barrister Musa Lawal Ozigi

Barrister Ozigin shi ne Sakatare Janar na Ƙungiyoyin Ƙwadago na Najeriya (TUC).

Shugaban TUC Quadri Olaleye ne ya tabbatar da mutuwar Barrister Ozigin yana mai cewa Jihar Kwara ta rasa shugabanta na TUC a harin.

Ya bayyana mamacin a matsayin mutum mai faran-faran da farin jinin jama’a.

Olaleye ya ce Barista ya tafi Kaduna ne don gabatar da wasu muhimman abubuwa a ranar Talata 29 ga watan Maris din 2022.

Wasu manya da suka sha da ƙyar

Nuhu Danja

Danja kwamishinan lafiya na Jihar Katsina na daga cikin waɗanda suka tsira a harin amma ya jikkata.

Ibrahim Almu Gafai na ma’aikatar lafiya ta Katsinan ya shaida wa manema labarai cewa an harbi kwamishinan ne a kafarsa inda har yatsunsa biyu na ƙafa suka cire.

A yanzu haka yana kwance a asibiti a Kaduna.

Alhaji Ibrahim Wakkala

Wakkala tsohon mataimakin gwamnan Jihar Zamfara ne a lokacin da Abdulaziz Yari ke mulki, kuma shi ma abin ya rutsa da shi.

Mai taimaka masa kan yada labarai Yusuf Idris ya ce an harbi maigidan nasa ne a ƙafa shi ma kuma a yanzu yana asibiti ana kula da shi.

Wakkala a gadon asibitin ya shaida wa BBC cewa ya gode wa Allah da Ya ceci rayuwarsa, kuma nan ba da jimawa ba za a yi masa tiyata a cire harsashin a ƙafarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here