WAEC ta Rike Sakamakon Wasu ɗalibai

An fitar da sakamakon jarrabawar kammala makarantun sakadire ta Afrika ta yamma wato WAEC da ɗalibai suka zana a wannan shekara.

Alƙalumman da hukumar shirya jarrabarwar ta fitar sun nuna cewa kaso 65 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarrabawar sun samu nasara.

Dalibai 1,549,740 ne suka yi rijista, yayin da 1,538,445 suka rubutata.

Sai dai an riƙe sakamakon ɗalibai 215,149, wato kaso 13 cikin 100 na yawan ɗaliban da suka rubuta jarrabawar saboda zargin satar amsa.

Baya ga Najeriya ana kuma gudanar da jarrabawar a ƙasashen da suka haɗar da Cote d’Ivoire, da Benin da Equatorial Guinea.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here