Wajen da ya fi Ko Ina Zafi a Duniya a Cikin Awa 24
An ayyana filin Arafa a matsayin wajen da ya fi ko ina zafi a duniya, a cewar Dr. Abdullah Al-Misnad, wani tsohon malamin yanayi a Jami’ar Al-Qassim ta Saudiyya.
Jaridar intanet ta Saudi Gazette ta rawaito cewa, farfesan, wanda tsohon shugaban kwamitin sauyin yanayi ne na Saudiyya, ya bayyana cewa filin Arafan ya kasance mafi zafin ne cikin awa 24 da suka wuce.
Al-Misnad ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa shafin da ke kula da yanayi a duniya na “El Dorado Weather” ne ya wallafa bayanan, inda ya ce ma’aunin zafi a Saudiyya ya kai digiri 43, inda ya zama mafi tsanani a duniya cikin awa 24.
Al-Misnad ya kuma ƙara birnin Abha a cikin waɗanda ba a yi zafi sosai ba cikin biranen Saudiyya, inda ya kai digiri 11 a ma’aunin salshiyas.
Filin Arafa tsarkakakken waje ne da Musulmai ke gabatar da ibadun Hajji da yake kusa da Makkah da Taif.
A ranar 31 ga watan Agustan 2021 sai da yanayin zafi a filin Arafa ya kai digiri 50 a ma’aunin salshiyas, mafi zafi da aka taɓa samu a duniya.
A watan Yunin bana kuwa, Kuwait ce ta samo mafi tsananin zafi a dunia a shekarar 2021, inda ta kai maki 53.2 na ma’aunin salshiyas.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here