Aliyu Magatakarda Wamakko ya Lashe Zaɓen Sanatan Sokoto ta Arewa
Tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya lashe zaɓen sanatan Sokoto ta Arewa, a zaɓen cike giɓi da aka gudanar jiya a wasu sassa na Najeriya.
Magatakarda ya samu nasara ne a kan mataimakin gwamnan Sokoto Mannir Muhammad Ɗan’iya.
Read Also:
Wamakko ya samu ƙuri’a 141,468 yayin da babban abokin takararsa Ɗan’iya ya samu 118,445 a zaɓen, wato bambancin ƙuri’a 23,023 tsakaninsu.
A baya dai, an bayyana zaɓen a matsayin wanda bai cika ba saboda zarge-zargen maguɗi da tashe-tashen hankula da amfani da ‘yan banga wajen tarwatsa zaɓe.
Wamakko ya yi gwamnan jihar Sokoto sau biyu, kuma a 2015 ya ci kujerar sanata ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Yanzu dai ana jiran sakamakon kujerar sanata daga shiyya biyu ta ɗan majalisar dattijai daga jihar Sokoto da suka rage.