Ƙungiyar WAMY da Gidauniyar Malam Inuwa Sunyi wa Mutane 2,700 Aikin Ido Kyauta Karo Na Biyu a Jigawa
A daidai lokacin da al’umma da dama ke yawo da jinyoyi kala-kala tare da su saboda yanayin rayuwar yau, ƙungiyar matasa musulmai ta Duniya, World Assembly Of Muslim Youth, (WAMY), da haɗin gwiwar Gidauniyar Malam Inuwa wacce ke ƙarƙashin jagorancin mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, (CCIE), a karo na biyu, sun ɗauki nauyin gudanar da ba da maganin ciwon Ido, raba gilashin ƙara ƙarfin ganin Ido, gami kuma da aikin tiyatar Ido kyauta a Jihar Jigawa domin tallafawa al’umma masu lalurar.
Aikin wanda aka gudanar da shi tsawon kusan mako guda a birnin Dutsen Jihar Jigawa, an yi wa jimillar mutane (636) aikin tiyatar, ya yin da aka ba wa jimillar mutane (600) gilashin ƙara ƙarfin gani, sai kuma jimillar mutum (1,500) waɗanda aka ba wa magungunan ciwon idon.
Read Also:
Bayan kammala aikin a wannan rana, an kuma gudanar da bikin karramawa na musamman ga Likitoci, ma’aikatan lafiya, gami da jami’an tsaro da sauran mutanen da su ka tallafa har aka kai ga samun sa’ar kammaluwar aikin cikin nasara.
Kana kuma, daga bisani gidauniyar ta Malam Inuwa ta shirya liyafa ta musamman domin karrama jami’an gidauniyar ta (WANY), Dakta Isham, da kuma Dakta Bihlali Abdallah, gami da sauran likitocin da su ka tallafa musu a aikin.
A dunƙule, wannan shi ne karo na biyu da aka samu haɗin gwiwa a tsakanin gidauniyar ta (WAMY) da kuma ta Malam Inuwan kan aikin Ido, ba da magani da gilashi kyauta a Jigawa. Hakan kuma shi ne ke zaman karo na uku da gidauniyar ta Malam Inuwa ta samar da irin wannan aikin ido na haɗin gwiwa a Jihar ta Jigawa duba da haɗin gwiwar da ta yi da ƙungiyar ƙasar Qatar da ta haɗakar jami’an lafiya na Duniya aka gudanar da aikin Gumel.
Ɗumbin jama’a da dama sun bayyana godiya da farin cikinsu gami da addu’ar fatan alkhairi. “Waɗanda su ka ɗauki nauyin wannan abu, Allah Ya saka musu da alkhairi, Allah Ya sa su gama lafiya, Allah Ya sa sakamakonsu gidan Aljannah,”. Cewar ɗaya daga cikin waɗanda su ka amfana da aikin, mai suna Alhaji Audu Ali, ɗan asalin yankin Warwaɗe Dam, da ke Dutse.