Bayan Wanke Ido da Fitsari: Mutum ya Kamu da Makanta
Wani mutum a Mozambique ya makance bayan ya yi amfani da maganin gargajiya da fitsari wajen warkar da ciwon ido.
Mutumin mai suna Babu Aiuba yana jinya a babban asibitin Quelimane a yanzu.
Ya shaida wa manema labarai na cikin gida cewa ya kamu da wata cuta ta ido a farkon wannan watan.
“Na wanke idona da sabulu da fitsari,” in ji shi.
Mista Aiuba ya ce wannan al’ada ce ta mutanen unguwar.
Sai dai hakan ya kara dagula masa ido, inda ta kai har ya rasa ganinsa.
Read Also:
Likitan ido Eugénia Cavele, ya ce amfani da magungunan gargajiya na sa cutar ta tsananta har zuwa ga makanta.
“Ina so in yi gargaɗi ga duk wanda ke da alamomi na ciwon ido da kada ya yi amfani da abubuwan da ba a tabbatar da su a kimiyyance ba, saboda hakan na iya haifar da makanta,” in ji Mista Cavele.
Wannan shi ne karo na farko da aka samu maganin gargajiya ya haifar da makanta tun bayan ɓullar wata cutar idanu a Mozambique.
A yanzu ciwon ya shafi kusan dukkanin lardunan Mozambique, ciki har da Maputo, babban birnin ƙasar.
Hukumomi sun kuma bayar da rahoton ɓullar cutar a gidan yari na lardin Maputo.
Akalla fursunonin gidan yarin 270 ne suka kamu da ita.
Cutar ta ciwon idanu ta kuma ɓarke a wasu ƙasashe da dama a gabashi da kudancin Afirka.