Ba Wasa Nake yi da Burina na Zama Shugaban Kasa ba – Tinubu ga Sarakunan Gargajiya
Tsohon gwamnan jihar Legas, Tinubu ya bayyana bukatarsa ta son gaje Buhari, inda yace ba da wasa yake takara ba
Ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wata ziyara jihar Edo domin neman goyon baya da albarkar sarakunan gargajiya
A bangare guda, basaraken gargajiya ya shawarci ‘ yan siyasa da su guji fadin abubuwan da ba za su iya ba lokutan kamfen
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Benin, Jihar Edo – Jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba wasa yake ba a burinsa na zama shugaban kasa, ya kara da cewa al’ummar kasar nan na bukatar shugaban da zaai kawo sauyi irin sa a 2023.
Read Also:
Tinubu wanda ya je Benin, babban birnin jihar Edo a karshen mako domin neman bakin wakilan APC gabanin fidda gwani, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Oba na Benin a fadarsa.
A cewar Tinubu:
“Ni ne wanda ya fi cancanta da dacewa na tsayawa takarar shugaban kasa da kuma jagorantar al’ummar kasar nan wajen magance matsalolin tattalin arziki da tsaro.”
Jam’iyyar APC ta tsayar da ranakun 29 da 30 ga watan Mayu domin gudanar da zabukan fidda gwani na shugaban kasa gabanin zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya ce:
“Ba wasa nake yi da burina na zama shugaban kasa ba, ina son zama shugaban kasa. Ina nan fadar ne don neman albarka da addu’arku na zama dan takarar jam’iyyar APC kuma a karshe na zama shugaban kasa. Na san ma’anar albarkar ku da yarjewarku.”
Da yake mayar da martani ga batun Tinubu, Oba na Benin, Oba Ewuare II, ya shawarci ’yan siyasa da su mayar da hankali kan manufofin da za su iya cimmawa a madadin jero abubuwan da ba za su iya cimma ba, rahoton Tribune Online.