Abubuwa Game da Wasan Tottenham da United
Tottenham za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na 33 a Premier League ranar Alhamis.
Tottenham tana mataki na bakwai a teburin Premier League da maki 53, ita kuwa United mai kwantan wasa biyu tana ta hudu mai maki 59 iri daya da na Newcastle United ta uku.
Da kyar idan golan Tottenham, Hugo Lloris zai buga karawar ta ranar Alhamis, sakamakon rauni da ya ji a kugu da ta kai an sauya shi ranar Lahadi.
Ben Davies da Clement Lenglet sun koma yin atisaye bayan jinya da suka yi, shi kuwa Lucas Moura ya gama hutun dakatar da shi wasa daya.
Dan kwallon Manchester United, Bruno Fernandes ya gurde kafa a lokacin fafatawar FA Cup da Brighton a Wembley.
Kyaftin Harry Maguire zai iya buga wasan, bayan hukuncin dakatarwa karawa daya da FA ta yi masa.
Wadanda ke jinya a United kawo yanzu sun hada da Alejandro Garnacho da Lisandro Martinez da Scott McTominay da Donny van de Beek da kuma Raphael Varane.
Tottenham ta nada Ryan Mason a matakin rikon kwarya karo na biyu da zai horar da kungiyar.
Tsohon dan kwallon Tottenham ya ja ragamar kungiyar ta ci wasa hudu aka doke shi uku.
Karawa tsakanin kungiyoyin biyu
Read Also:
Tottenham ta yi rashin nasara a wasa hudu a jere a Premier League a hannun Manchester United, rashin nasara mai yawa a hannun United tun bayan bakwai a jere da aka doke Tottenham tsakanin Satumbar 2001 zuwa Satumbar 2004.
Wasa uku Tottenham ta yi nasara a gida daga 21 baya da ta karbi bakuncin United da canjaras bakwai da rashin nasara 11 a manyan karawa.
United na fatan cin Tottenham karo na 40 a Premier League.
Ranar 19 ga watan Oktoba United ta doke Tottenham 2-0 a wasan farko a Premier League ta bana.
Tottenham
Tottenham ta yi rashin nasara a wasa biyu aka dura mata kwallo tara.
An zura wa Tottenham kwallo 28 a Premier League a 2023, wadda aka fi durawa kwallaye tun shiga shekarar nan ita ce Leeds United mai 33 a raga.
Karawa daya Tottenham ta ci daga tara a Premier League da kungiyoyin da ke ‘yan bakwan farko a teburi aka doke ta wasa takwas daga ciki.
Saura kwallo daya Harry Kane ya ci 100 Premier League a gida.
Manchester United
Ba a doke Manchester United a wasa bakwai da ta kara a tsakiyar mako ba, wadda ta ci biyar da canjaras biyu.
United na fatan cin wasa na hudu a jere ba tare da an zura mata kwallo a raga ba a karon farko tun bayan bajintar da ta yi karkashin Sir Alex Ferguson daga Fabrairu zuwa Marisn din 2013.
Kungiyar da Ten Hag ke jan ragama ta sha kashi a wasa biyar da ta fuskaci ‘yan bakwai a kan teburi aka zura mata kwallo 21 a raga.
Idan aka doke United zai zama na 200 kenan a Premier League.
David de Gea zai tsare ragar United karo na 500 a Premier League.