Yadda Wasu Jam’iyyu Suka Rasa Mambobin su
Mambobin jam’iyyun PDP da APGA fiye da 500 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Abia.
Taron ya samu halartan Sanata Orji Kalu da shugaban APC a jihar Abia, Donatus Nwapka.
Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya sanar da komawarsa jam’iyya mai mulki.
Guguwar sauyin sheka ya yi wa masu adawa tsinke yayina mambobin jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da All Grand Progressives Alliance (APGA) suka koma All Progressives Congress (APC) mai mulki.
A cewar The Nation, sauyin shekar ya gudana ne a gudunmar Ikwun da ke Ihechiowa a karamar hukumar Arochukwu na jihar Abia a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.
An tattaro cewa masu sauya shekar sun yayyaga katin kasancewarsu yayan tsoffin jam’iyyunsu a yayin bikin wanda ya samu halartan Orji Uzor Kalu, Shugaban bulaliyar majalisar dattawa da shugaban APC a jihar, Donatus Nwapka.
Read Also:
Da yake magana a taron, Kalu ya yaba ma sabbin mambobin a kan wannan mataki da suka dauka sannan ya nuna yakinin cewa APC za ta lashe jihar Abia a 2023.
A cewar dan majalisar, sauyin shekar ya nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na yiwa jihar da yankin kudu maso gabas gaba daya kokari.
Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya koma jam’iyya mai mulki, lamarin da ke ci gaba da haddasa cece-kuce.
A gefe guda, rashin sanar da yankin da jam’iyyar PDP za ta mikawa tikitin takarar shugaban kasarta a 2023, ya sa shugabannin jam’iyyar sun fara juyawa juna baya.
The Nation ta ruwaito cewa kwamitin masu ruwa da tsaki ta NWC na PDP na fuskantar matsin lamba domin kaddamar da matsayinsa kan tsarin mika mulki na yanka-yanka.
Legit.ng ta tattaro cewa karin gwamnoni da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar, suna barazanar sauya sheka idan shugabancin jam’iyyar ya ki nuna jajircewarsa wajen mika tikitin shugaban kasa ga yankin kudu.