Watan da Za a Fara Kamfe – INEC

 

Hukumar zabe mai cin gashin kai a Najeriya, INEC ta ce nan da kusan watanni shida za a fara kamfe.

Daga ranar 28 ga watan Satumba za a bada dama domin a fara yakin neman zaben shugaban kasa.

Zuwa Watan Maris 2023 za a rufe kofar kamfe, a jira ranar zaben jihohi, majalisa da shugaban kasa.

Kaduna – A lokacin da aka fara hango hadarin siyasar 2023, hukumar zabe mai zaman kanta watau INEC ta tsaida lokacin da za a soma kamfe a Najeriya.

Jaridar Daily Trust a wani rahoto da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce INEC ta sa lokacin da za a fara yakin neman takarar gwamna, majalisa da na shugaban kasa.

Hukumar zabe ta kasa ta ce daga ranar Laraba, 28 ga watan Satumban 2022 za a soma yakin neman zaben shugaban kasa da na kujerun majalisar tarayya.

A wannan lokaci ne masu harin kujerar shugaban kasa da masu neman zama Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilan tarayya za su fara kamfe a fadin kasar nan.

INEC ta kuma tsaoda ranar 12 ga watan Oktoban 2022 a matsayin lokacin da za a iya fara yawon yakin neman takarar gwamna da na majalisar dokoki a jihohi.

Babbar kwamishinar zabe ta shiyyar Kaduna, Hajiya Asmau Sani Maikudi ta shaidawa manema labarai wannan a lokacin da ta zanta da su a yammacin Laraba.

Yaushe za a gama kamfe?

Da take jawabi a Kaduna, Asmau Maikudi ta bayyana cewa daga ranar 23 ga watan Fubrairun 2023, an rufe yakin zaben ‘yan majalisa da na shugaban kasa.

Haka zalika bayan 9 ga watan Maris 2023, babu ‘dan takarar gwamna ko ‘dan majalisar dokoki da zai cigaba da kamfe. Za ayi kusan watanni biyar ana yakin zabe.

Ana cigaba da shirin 2023

Rahoton ya kuma tabbatar da cewa hukumar INEC ta kara adadin rumfunan zabe a Najeriya. Daga rumfuna 5012 da aka yi amfani da su a 2019, yanzu akwai 8012.

A jawabin na jami’ar hukumar zaben, an kuma fahimci mutane su na cigaba da yin rajistar samun katin zabe na kasa. A yanzu mutane 236,855 sun fara yin rajista.

Zuwa farkon makon nan, mutane 84,335 ne kurum suka kammala rajistar samun katin kada kuri’ar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here