Jerin Wayoyin da Manhaja Whatsapp za ta Daina Aiki a kansu a 2023
Miliyoyin wayoyi a fadin duniya na gab da daina WhatsApp daga Junairun sabuwar shekara.
Masu amfani da wadannan wayoyi da zasu daina aiki su shirya tanadar sabuwar waya tun da wuri.
Manhajar WhatsApp ta shahara cikin al’umma inda kusan kowa na amfani da ita wajen hira.
A cewar Wikipedia, sama da mutane bilyan 2 na amfani da WhatsApp a fadin duniya.
Manhajar WhatsApp za ta daina aiki a wayoyi da dama nan da ranar 1 ga watan Junairu 2023.
A sakon da ta aikewa dimbin masu amfani da WhatsApp, ta bayyana cewa zasu daina amfani da manhajar kan wasu wayoyi guda 47.
A cewar jawabin, wayoyin Android da Iphone duka wannan zai shafa. A shafin FAQ dinta, WhatsApp tace:
“Wayoyi da manhajoji kan canja akai-akai, saboda haka lokaci bayan lokaci mukan sake nazari kan manhajojinmu kuma muyi sauyi.”
“Kamar sauran kamfanonin sadarwa, Muna zaben wayoyin da manhajarmu zata daina aiki akansu ne dubi ga tsufarsu da kuma karancin masu amfani da su.”
Read Also:
“Wadannan wayoyi mafi akasari basu samun kariya, kuma karfinsu ya yi raunin da WhatsAPP ba zata iya aiki a kansu ba.”
Ga jerin wayoyin da WhatsApp zata daina aiki
iPhone 5
iPhone 5c
Archos 53 Platinum
Grand S Flex ZTE
Grand X Quad V987 ZTE
HTC Desire 500
Huawei Ascend D
Huawei Ascend D1
Huawei Ascend D2
Huawei Ascend G740
Huawei Ascend Mate
Huawei Ascend P1
Quad XL
Lenovo A820
LG Enact
LG Lucid 2
LG Optimus 4X HD
LG Optimus F3
LG Optimus F3Q
LG Optimus F5
LG Optimus F6
LG Optimus F7
LG Optimus L2 II
LG Optimus L3 II
LG Optimus L3 II Dual
LG Optimus L4 II
LG Optimus L4 II Dual
LG Optimus L5
LG Optimus L5 Dual
LG Optimus L5
LG Optimus L7
LG Optimus L7 II
LG Optimus L7 II Dual
LG Optimus Nitro HD
Memo ZTE V956
Samsung Galaxy Ace 2
Samsung Galaxy Core
Samsung Galaxy S2
Samsung Galaxy S3 mini
Samsung Galaxy Trend II
Samsung Galaxy Trend Lite
Samsung Galaxy Xcover 2
Sony Xperia Arc S
Sony Xperia miro
Sony Xperia Neo L
Wiko Cink Five
Wiko Darknight ZT