Sabon Ministan Birnin Tarayya, Wike ya yi Barazanar Rusa Gidaje
Sabon ministan babban birnin tarayyar Najeriya – Abuja, Nyesom Wike, ya yi barazanar fara rusa gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba.
Wike ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi domin soma aiki.
Read Also:
“Idan kun gina gidajenku a wuraren da aka saba ka’ida, sai an rusa su,” in ji Wike.
Tsohon gwamnan Ribas din yana cikin ministoci 45 da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da su a fadarsa da ke Abuja.
Wike ya sha alwashin yin tir da tsarin da ke kawo cikas ga taswirar babban birnin tarayyar.