Wike ya yi Kira ga Matasa a Babban Birnin Tarayya da Kada su Shiga Zanga-Zanga

 

Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike ya yi kira ga matasa a babban birnin ƙasar da kada su shiga zanga-zangar da ake shirin yi kan adawa da tsadar rayuwa daga ranar 1 ga watan Agusta.

A makon da ya gabata ne tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce babu zanga-zanga da za a yi a babban birnin tarayya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga matasan da suka sha alwashin gudanar da fareti a dandalin Eagle Square.

Sai dai ga dukkan alamu ministan ya sassauta a wani taron masu ruwa da tsaki na matasa da aka yi karamar hukumar Bwari ranar Litinin, inda ya buƙace su da su bayyana matsalolinsu sannan su dakatar da shirin fita zanga-zanga.

Wadanda suka halarci taron sun haɗa da shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin addini da kuma wakilan ƙungiyoyin mata da matasa.

Ministan ya yaba wa waɗanda suka halarci taron da kuma rungumar tattaunawa, inda ya ƙara da cewa shugaba Bola Tinubu na iya ƙoƙarinsa wajen ciyar da ƙasar gaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here